Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Abin Da Ya Sa Muka Hana Ayyukan Jari-Bola A Borno: Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya bada
umarnin dakatar da ayyukan ‘yan jari-bola a fadin jihar, yayin
wata ziyara da ya kai yankin Bulumkutu a ranar Litinin da ta
gabata.

Babagana Zulum dai ya ci karo da wasu tarin karafa na gwamnati da ake zargin masu sana’ar jari-bola ne su ka lalata su, kuma dakatarwar ta shafi kananan hukumomi 27 da ke fadin jihar Borno.

Gwamna Zulum, ya ce a shekarun baya masu irin wannan sana’a da dama sun rasa rayukan su, sakamakon hare-haren mayakan Boko-Haram saboda su na zuwa yankunan da babu mutane sosai domin barnata kayayyaki.

Haka kuma, gwamnan ya ce ana zargin wasu daga cikin ‘yan jari-bola da sace dukiyoyin gwamnati da na jama’a, ya na mai cewa, irin wadannan sace-sacen na iya kawo cikas ga ayyukan gwamnatocin jihohi da na tarayya.

A karshe ya ce zai sa hannu a kan wata doka da za ta hana duk wani nau’in ayyukan ‘yan jari-bola a jihar Borno, ya na mai cewa an bada umarnin ne domin a tsabtace harkokin kasuwanci da kuma kare rayukan su kan su masu sana’ar jari- bola a fadin jihar.

Exit mobile version