Shugaban kwamitin kuɗin da gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya yi ƙarin haske kan daftarin dokar gyaran haraji wanda shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa,
inda ya ce an tsara daftarin ne ta yadda za a rage wa ma’aikata kaso 90% na harajin da suke biya.
Mista Oyedele ya yi wannan ƙarin haske ne a jiya Laraba a yayin amsa gayyatar majalisar dattawa domin gamsar da ita kan amincewa da wannan daftari.
Ya ce daftarin dokar an yi shi ne domin sake duba fasalin harajin VAT domin daidaita abin da kowacce jiha ya kamata ta samu ta la’akari da abin da ake samarwa a jihar.
A watanni biyu da suka wuce ne, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya aike wa majalisun Najeriya, daftarin dokar gyaran fasalin harajin na 2024.

