Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zullumi Yayin Da Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Kan Makomar Abubakar Malami

Babbar kotun Tarayya da ke Abuja, ta dage sauraran karar da
aka shigar a kan tsohon ministan shari’a Abubakar Malami
bisa zargin karfa-karfa.

Alkalin kotun mai shari’a Oluyemisi Adelaja, ya dage sauraren karar ne zuwa ranar 17 ga watan Oktoba domin a ba wanda ake kara damar shiryawa.

A cikin karar dai, dan kasuwar mai suna Cecil wanda dillalin filaye ne a birnin Abuja, ya ce Abubakar Malami ya tilasta ma shi ba wata ma’aikaciyar gwamnati mai suna Asabe Waziri gidaje biyu a yankin Maitama.

Ya ce Abubakar Malami, ya kuma ya tilasta ma shi ba matar kadarar da ta kai Naira miliyan 130, duk da cewa maganar ta na kotu, inda Cecil ya ce Malami ya shiga tsakani a matsalar kamfanin sa da Waziri.

Cecil ya kara da cewa, Malami ya umarci jami’an tsaron sa su cigaba da cin zarafin sa lokacin da ya ke minista, kuma da sanin Malami cewa Waziri ta shafe watanni takwas a gidan kafin kotu ta fitar da ita.

Exit mobile version