Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ta girke ƙarin jami’an tsaro domin tabbatar da komai ya tafi daidai gabanin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa manema labarai hakan yau a birnin Yola.
SP Suleiman Nguroje, ya ce sun bukaci jami’an su nuna ƙwarewa da kuma mutunta ‘yancin dan adam yayin gudanar da aiki.
Kakakin ‘yan sandan ya ce ƙarin jami’ai da aka girke sun haɗa da rundunonin jami’an tsaro da jami’an sashin ƴaki da ta’addanci da kuma motocin samame.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa shugaba Buhari zai ziyarci jihar ne a ranar Litinin domin kaddamar da ƴakin neman zaɓen ‘yar takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Binani.