Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ziyarar Aiki: Buhari Ya Tafi Kasar Laberia

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tafi kasar Liberia domin halartar bikin taya kasar murnar bikin cika shekaru da 172 da samun ‘yanci da kuma karbar wata kyauta ta musamman.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, wacce ta fito daga fadar shugaban kasa.

Shugaban kasa Buhari ne babban bako a wurin taron, sannan zai karbi kyautar girmamawa mafi daraja da kasar Libria ke ba mutane masu daraja da mutunci.

Gwamnatin kasar Liberia ce ke bayar da kyautar ga mutane masu daraja da suka taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, da gwamnati da addini da kimiyya da kasuwanci da aikin jin kai da jarumta da sadaukarwa da makamantan su.

Shugaba Buhari ya sami rakiyar gwamnoni da suka hada da Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara, Mai Mala Buni na jihar Yobe, da kuma sakataren ma’aikatar harkokin waje, Ambasada Mustapha Sulaiman, da sauran manyan kusoshin gwamnati.A yau ne ake sa ran shugaban kasa Muhammad Buhari zai dawo

Exit mobile version