Tsohon shugaban kasar Zimbabwe na farko bayan ta sami ‘yancin kai Robert Mugabe ya mutu yana da shekara 95.
Iyalansa sun ce ya mutu ne bayan wata jinya da ya yi.
An hambarar da Mugabe daga mulki, ne a wani juyin mulki da aka yi masa a watan Nuwambar 2017, wanda ya kawo karshen mulkinsa na shekara 30.
An haife shi a ranar 21 ga watan Fabrairun 1924 a lokacin sunan kasar Rhodesia.
Kuma an zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar ZANU a 1973 a lokacin yana tsare a kurkuku, kuma yana cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar.