Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zargin Zagon-Kasa: Abdul-Aziz Yari Ya Kalubalanci Rahoton Kwamitin APC

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya bayyana rahoton da kwamitin mutane biyar na jam’iyyar APC su ka gabatar, wanda ke zargin sa da yi wa jam’iyyar zagon kasa a matsayin raini da kuma tozarci a gare shi.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan Ibrahim Dosara, ya ce ikirarin kwamitin da kuma abubuwan da ake wallafawa a kafofin yada labarai ba su da fa’ida, sun kuma saba ma hukunci da umurnin kotu.

Abdul-Aziz Yari, ya ce rahoton kwamitin ya haddasa tarin tozarci da batanci gare shi.

Rahoton kwamitin dai ya zargin cewa, rawar da Abdul-Aziz Yari da Lawal Shu’aibu su ka taka a zaben shekara ta 2019 ya taimaka wajen rashin nasarar jam’iyyar a jihar Zamfara.

Exit mobile version