Home Home Zargin Yaudara: ‘Yan Majalisa Sun Titsiye Shugaban ASUU Kan Gbajabiamila

Zargin Yaudara: ‘Yan Majalisa Sun Titsiye Shugaban ASUU Kan Gbajabiamila

73
0
Wasu ‘yan majalisar wakilai sun titseye shugaban ƙungiyar malaman jami’o’ na Najeriya ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, kan wasu zarge-zarge da ya yi na cewa shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya yaudari ƙungiyar wajen jan hankalin ta domin janyewa daga yajin aikin da ta shafe watanni tana yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a wata hira da shugaban ASUUn ya yi da wata jarida a ranar talata ya zargi Gbajabiamila da cewa ya yi amfani da yaudara wajen sanya ƙungiyar janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa a watan Oktoba, ta hanyar rubutaccen alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta biya malaman duk albashin watannin da ta riƙe musu ba tare da ɓata lokaci ba.

Yayin da yake mayar da martani game da zargin na shugaban ASUU a Abuja, mai magana da yawun majalisar wakilan Benjamin Okezie Kalu, ya ce babu inda shugaban majalisar ya yi alƙawarin warware matsalar albashin da malaman ke bin gwamnatin tarayya bashi.

Ya ce majalisar wakilan ta taimaka ne kawai wajen kawo ƙarshen yajin aikin, ta hanyar yin ƙoƙari wajen inganta albashin malaman jami’o’i tare da taimakawa wajen samar da kuɗin inganta jami’o’in na ƙasa.

Leave a Reply