Hukumar hana zambar kudi da karya tattalin arzikin kasa EFCC ta kama Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky saboda zargin sa da wulaƙanta takardar naira.
EFCC ta wallafa a shafin ta na fesbuk cewa ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin damman takardun naira a bikin nuna wani fim da aka yi ranar 24 ga watan Maris a jihar Legas.
A baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.
A cewar hukumar, Bobrisky na ofishinta na Legas domin amsa tambayoyi.
EFCC ta ce ba da daɗewa ba za a gurfanar da Bobrisky a gaban kotu.