Home Labaru Zargin Tauye Haƙƙi: Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Kanu Kan DSS

Zargin Tauye Haƙƙi: Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Kanu Kan DSS

83
0

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da ƙarar
da Shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu fafutukar kafa
ƙasar Biyafar Nnamdi Kanu ya shigar a kan Hukumar Tsaro ta
Farin Kaya DSS.

A cikin hukuncin da ya yanke, Mai shari’a James Omotosho ya ce ƙarar Nnamdi Kanu ba ta da inganci, kuma ya kamata a yi watsi da ita.

A cikin ƙarar da Nnamdi Kanu ya shigar, ya yi zargin cewa hukumar DSS ta na cin zarafinsa a lokuta daban-daban, ciki har da hana shi haƙƙin sa na sanya duk suturar da ya ga dama musamman rigar gargajiya ta qabilar Igbo da ake kira “Isi- Agu,”.

Nnamdi Kanu ya yi zargin cewa, jami’an tsaron da ya ke hannun su sun ba sauran fursunonin da ke hannun su ’yancin zaɓe ko sanya duk tufafin da su ka ga dama, amma shi an hana shi hakan.

Sai dai a takardar ƙarar da hukumar DSS da shugaban ta su ka shigar, sun buƙaci kotun ta yi watsi da ikirarin Nnamdi Kanu., inda su k ace jami’an su ba su taɓa azabtar da shi ba lokacin da su ke tsare da shi ba.

Leave a Reply