Kotun ɗaukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da Felix
Okonkwo lauyan da ke kare Nnamdi Kanu, jagoran masu
fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) da ake tsare da shi ya
shigar kan zargin kama shi da tsare shi da ‘yan sanda da jami’an
tsaron farin kaya suka yi ba bisa ka’ida ba.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Okon Abang ya yi watsi da ɗaukaka karar, inda ya bayyana cewa ba shi da inganci. Ya yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya kasa nuna rashin adalci a hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan lamarin.
Abang ya jaddada cewa, hujjojin bidiyon da masu karar suka gabatar a lokacin shari’ar ba su nuna wani hannun jami’an DSS ba a wurin da aka kama su a gidan Ifeanyi Ejiofor a jihar Anambra.
Dangane da diyyar naira miliyan biyu da aka ce ƴandan da DSS su bayar, mai shari’a Abang ya ki amincewa da hujjar wadanda suka shigar da kara na cewa adadin kuɗin bai wadatar ba, inda ya ce hurumin tantance diyya ya rataya a wuyan alkali ne kawai.