Home Labaru Zargin Safarar Kwaya: An Yi Zanga-Zangar Neman Saudiyya Ta Saki Zainab Aliyu

Zargin Safarar Kwaya: An Yi Zanga-Zangar Neman Saudiyya Ta Saki Zainab Aliyu

407
0

Wasu dalibai sun gudanar da zanga-zangar neman sakin ‘yar Nijeriyar mai suna Zainab Aliyu da ke tsare a kasar Saudiyya.

Daliban dai sun yi zanga-zangar ne daga Jami’ar tunawa da Yusuf Maitama Sule da ke birnin Kano, inda su ka bukaci a gaggauta sakin ta ba tare da bata lokaci ba.

Yanzu haka dai, hukumomin kasar Saudiyya sun saki Zainab Aliyu kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasa a kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmed ya bayyana wa manema labarai.

Wata kwakkwarar majiya ta ce an rubuta wa jami’an gwamnatin Saudiyya takardu kamar yadda aka harkokin difilomasiyya.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari’a Abubakar Malami ya shiga maganar, ya kuma tabbatar da an saki dalibar an kuma maido ta Nijeriya.

Sai dai tuni hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta ce wasu ma’aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano su ka sanya mata kwayar a cikin jakar ta.