Tsohon gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar, ya amsa bayyana ma wata babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa ya kashe naira biliyan 8 da rabi ana saura kwanaki biyu kacal ya mika mulki.
Sai dai ya shaida wa kotun cewa, ya kashe kudaden ne domin biyan wasu kamfanoni da su ka yi kwangiloli a jihar lokacin ya na kan mulki.
Ya ce ya biya kamfanonin adadin kudaden ne a ranar da jihar Bauchi ta same su daga babban bankin Nijeriya CBN, a matsayin biyan bashin ayyukan gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar ta yi.
Tsohon
gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin lauyan sa Basil Kpenkpen, a cikin wata
takarda da ya mika wa kotun domin kare kan sa daga tuhumar badakalar naira biliyan
19 da miliyan 900 da hukumar EFCC ke yi ma shi.