Home Labaru Zargin Maita: Mahaifi Ya Banka Wa ‘Ya’yan Sa Biyu Wuta A Jihar...

Zargin Maita: Mahaifi Ya Banka Wa ‘Ya’yan Sa Biyu Wuta A Jihar Filato

556
0

Rundunar ‘yan sandata jihar Filato, ta tabbatar da yadda wani mahaifi ya banka wa ‘ya’yan sa biyu wuta bayan ya zarge su da maita.

Nyam Choji, wanda dan asalin kauyen Shen ne da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, ya banka wa ‘ya’yan sa biyu wuta ne bayan ya zarge su da maita.

Mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar ASP Uba Gabriel ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce daga bayanan da su ka samu, mahaifin yaran da ‘ya’yan mai Unguwar yankin sun kasance su na wannan harka a yankin, sannan suna nan da yawa kuma sun sa a bankado su.

Sai dai a cikin wata sanarwa da da ta fitar, kungiyar mata ‘yan jarida ta kushe wannan lamari, ta na mai kwatanta hakan da take hakkin kananan yara, sannan ta bukaci Gwamna Simon Lalong ya bibiyi lamarin tare da tabbatar da an yi wa yaran adalci.

Leave a Reply