Sufeton Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya nemi a dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda bisa zargin karɓar cin hanci da ‘yan sandan Amurka ke yi masa.
Kazalika, IGP ɗin ya kafa wani kwamati na mutum huɗu ƙarƙashin jagorancin DIG Joseph Egbunike wanda zai binciki zargin da ake yi wa Abba Kyari mai muƙamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).
Usman Alkali ya bayar da shawarar dakatarwar ce cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ranar Asabar, yana mai cewa matakin “ɗaya ne daga cikin matakan ladaftarwa na rundunar ‘yan sanda”.
Ana zargin Abba Kyari da karɓar rashawa a hannun matashi ɗan Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, domin kamawa da kuma muzguna wa wani abokin harkarsa. Sai dai Kyari ya musanta zargin.
Hushpuppy ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar ce yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane.
Sai dai rundunar ta ce har yanzu tana ɗaukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa.
Kuna iya karanta cikakken labarin a nan: