Home Labaru Ilimi Zargin Fasikanci: Jami’ar Legas Ta Sake Dakatar Da Wani Malami A Kan...

Zargin Fasikanci: Jami’ar Legas Ta Sake Dakatar Da Wani Malami A Kan Neman Mata

495
0

Jami’ar Legas ta sake dakatar da wani malamin ta, sakamakon binciken da kafar yada labarai ta BBC ta yi, inda aka nuna yadda ake cin zarafin dalibai mata a jami’o’i biyu da su ka yi fice a yankin Afirka ta yamma.

Yayin binciken dai, an nuna Dakta Samuel Oladipo ya na kokarin ribatar ‘yar jaridar da ta yi shigar-burtu a matsayin mai neman gurbin shiga jami’ar.

Dakta Samuel, shi ne mutum na hudu kuma na karshe da jami’ar ta kora, tun bayan tona asirin su da binciken na BBC ya yi.

Sanarwar dai, ta na zuwa ne bayan da jami’ar Ghana ta ce za ta dakatar da malaman ta biyu da aka gani a cikin binciken na BBC, inda su ke kokarin neman wadanda su ka badda-kama a matsayin dalibai.Malaman uku da aka dakatar sun hada da Dakta Oladipo, da Farfesa Ransford Gyampo, da kuma Dakta Paul Kwame Butakor, amma dukkan su sun musanta zarge-zargen da jami’ar ta Legas ke yi masu.

Leave a Reply