Yan Sanda a Jamhuriyar Benin sun yi nasar capke wasu ‘yan Najeriya biyu dake kokarin kai hari da niyar fasa wani banki dake garin Bohicon dake tsakiyar kasar.
Bayan amsa wasu daga cikin tambayoyin masu bincike mutanen da ‘yan sanda suka kama sun bayyana cewa su shida ne suka shirya kai wannan hari, kuma sun riga sun shirya tsaf don aikata wannan fashi kamar dai yada suka tsara a baya.
‘Yan Sanda sun kadammar da bincike yanzu haka a wasu manyan biranen kasar don gano sauren mutanen dake aiki cikin wannan kungiya a cewar kakakin yan Sandan garin Bohicon.