Tsohon gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya gaskata zargin da Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya yi, cewa akwai gwamnonin da ke fakewa da karya ko gaskiyar matsalar tsaro su na sace kudaden jama’a.
Bafarawa ya jaddada zargin da Magu ya yi, lokacin da ya yi taron manema labarai a kan shirye-shiryen gudanar da Taron Makomar Tsaro A Nijeriya da Gidauniyar Attahiru Bafarawa za ta shirya.
Tsohon gwamnan ya ce, kamata ya yi gwamnonin yanzu su dauki darasi daga gare su da su ka yi mulki a baya, su tsaya su dubi yaya wasun su su ke a halin yanzu.
Ya ce duk abin da ka tara zai kare in dai ba ta hanyar gaskiya ka tara shi ba, ya na mai kuka da yadda gwamna zai kasa gyara firamare da sakandaren da ’ya’yan talakawa ke karatu, amma zai tura na shi ’ya’yan su yi karatu a kasashen waje.
Bafarawa ya cigaba da cewa, da ya ke an yi duk abubuwan a kan hanyar rashin rike amana, sai ‘ya’yan gwamnonin su fita waje karatu amma a karshe su zama ‘yan kwaya.