Home Labaru Zargin Cin Hanci: Alkali Ya Janye Daga Shari’ar Sowore Da Hukumar DSS

Zargin Cin Hanci: Alkali Ya Janye Daga Shari’ar Sowore Da Hukumar DSS

481
0
Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore - Malami
Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore - Malami

Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya janye daga karar da hukumar tsaro ta farin hula DSS ta shigar a kan shugaban gangamin juyin-juya-hali Omoyele Sowore.

Omoyele Sowore dai ya bukaci kotun ta umurci hukumar DSS ta sakeshi.

Sai dai Alkalin kotun ya janye daga shari’ar ne bayan zargin da ake yi ma shi na karbar cin hanci.

Tun lokacin da hukumar DSS ta sake kama shi sa’o’i kadan bayan sakin shi na farko, hukumar ba ta bayyana ainihin dalilan ta na aikata hakan ba, sannan ba ta tuhumi Sowore da wani sabon laifi ba.