Hukumar ta ce ta kama fitaccen mai amfani da shafukan sada zumuntar nan da aka fi sani da G-Fresh
Babban daraktan hukumar Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar wa manema labarai kan kama matashin.
Hukumar ta kama shi bayan jerin gargaɗin da ta yi masa sakamakon abubuwan da yake wallafawa a shafukan sa.
Yakara da cewa sun kama shi ne bayan tarin gargaɗinda muka sha yi masa kan abubuwan na baɗala da rashin kunya,
Abba Sufi ya ce hukumar Hisba za ta gurfanar da shi matashin a gaban kotu ranar Litinin
Al’amen G-Fresh dai ya yi fice a shafukan sada zumunta musamman TikTok, inda yake wallafa bidiyoyin,
lamarin da ya sa hukumar Hisbar ta ce ta yi masa gargadi da nasiha amma bai ɗauka ba.