Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zargin Badakala: Kwamitin Salami Ya Yi Alkawarin Sauraron Magu

Kwamitin fadar shugaban kasa da ke binciken Shugaban hukumar EFCC da aka dakatar Ibrahim Magu, ya ce zai tabbatar da ganin ya saurare shi,  sai dai kwamitin ya ki amsa bukatar Magu na neman a nadi zaman da za su yi a faifan bidiyo.

A cewar kwamitin wanda Ayo Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara ke jagoranta  bai san manufar Magu, na neman a nadi zaman ba.

A yayin zaman, Wata majiya daga kwamitin ta sanar da The Cable cewa kwamitin ya ki amincewa da nadar al’amarin a bidiyo, amma an tabbatar masa da cewa za a saurare sa.

Ayo Salami, ya ce kwamitin ko EFCC ba gurfanar da Magu suka yi ba domin ba wurin gurfanarwa bane, kwamiti ne kai da ke da alhakin bincike.

An kama Magu ne tare da tsaresa a ranar 6 ga watan Yulin 2020, bayan kiran gaggawa da kwamitin fadar shugaban kasar ta yi masa.

Antoni janar na tarayya kuma ministan shari’a ne ya mika korafi gaban shugaban kasa a kan wasu jerin zargi da ake ma Magu.

Exit mobile version