Home Labaru Zargi: Atiku Ya Ce Gwamnati Na Sace Mutane

Zargi: Atiku Ya Ce Gwamnati Na Sace Mutane

373
0
Atiku Abubakar, Tsohon mataimakin Shugaban Kasa
Atiku Abubakar, Tsohon mataimakin Shugaban Kasa

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben kasar na 2019, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta na fakewa da sunan kame ta na sace mutane ta na garkuwa da su.

Atiku Abubakar, ya bayyana haka ne a kafar sadarwar sa ta Tweeter a karshen mako, inda ya yi nuni da cewa, a na yi ne domin a tauye wa ’yan kasa hakkin su na bayyana albarkacin bakin su.

Atiku Abubakar, ya ce’yancin fadar albarkacin baki ba wai kawai kundin tsarin mulki ya tabbatar da shi ba ne kadai, ya na ma daga cikin wani ginshiki na shika shikan dimukradiyya.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar da Atiku ya bada waccan sanarwar jami’an tsaro sun kama jagoran juyin juyin hali Omoyele Sowere, wanda shi ne mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, wanda kuma shi ma dan takarar shugaban kasa ne a 2019.

Bugu da kari, gabanin wannan lokaci ne a ka sace wani magoyin bayan daya daga cikin wadanda su ka nemi takarar shugabancin kasar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Abubakar Idris, wanda a ka fi sani da Dadiyata a yanar gizo.

A rahotannin farko da a ka samu, jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian ta yi zargin cewa jami’an tsaro ne su ka kama shi, amma sun karyata rahoton hakan.