Home Labaru Zargi: APC Da Ganduje Na Neman Sauya Alkalan Shari’ar Zaben 2019 –...

Zargi: APC Da Ganduje Na Neman Sauya Alkalan Shari’ar Zaben 2019 – PDP

509
0

Jam’iyyar PDP ta ce akwai shirin da jam’iyyar APC da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ke yi na sauya Alkalan shari’ar karar zaben shekara ta 2019.

PDP dai ta zargi APC da gwamnatin Kano da yunkurin sauya Alkalan da za su saurari karar zaben gwamnan jihar da aka daukaka a gaban kotun daukaka kara da ke Kaduna.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya ce gwamnatin Ganduje ta na kokarin sauya Alkalan da aka zaba su saurari karar zaben jihar da wasu Alkalai na dabam.

Ya ce APC ta na son maye guraben Alkalan da kotun ta zaba ne da wasu Alkalan, wadanda za su yi wa gwamnati mai-ci aiki a karar da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shigar.

Leave a Reply