Home Labaru Zangon Mulki Na 2: Jonathan Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Cigaba Da...

Zangon Mulki Na 2: Jonathan Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Cigaba Da Hakuri

330
0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su cigaba da hakuri yayin da Nijeriya ke cika shekaru 20 da fara mulkin farar hula.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da shugaba Buhari ya ke kokarin shiga wa’adin mulki na biyu, Jonathan ya taya Nijeriya murna a kan ci-gaban da ake samu ta fuskar mulkin dimokradiyya.

Good Luck Jonathan, ya kuma roki ‘yan Nijeriya kada su fidda rai, duk da a yanzu Nijeriya ta na fama da matsalar tsaro da rashin aikin yi ga matasa.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa, Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo ba su halarci bikin rantsar da shugaba Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Leave a Reply