Home Labaru Zango Na Biyu: Shugaba Buhari Ya Bar Ministoci Cikin Zullumi

Zango Na Biyu: Shugaba Buhari Ya Bar Ministoci Cikin Zullumi

536
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Yayin da ya rage saura kwanaki kadan a sake rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Nijeriya karo na biyu, tuni ministocin sa sun kara kaimin kamun kafa wajen makusanta shugaba Buhari domin ya sake tafiya da su a zangon mulkin sa na biyu.

Rahotanni sun ce a kalla kashi 70 cikin 100 na ministocin Buhari sun bar ayyukan su domin ci-gaba da fafutukar ganin sun samu komawa a kan mukaman su.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce, ministocin sun shiga kamun kafa ne saboda sun san a wannan karon shugaba Buhari ba zai dauki dogon lokaci wajen nada ministocin da za su yi aiki da shi ba.

Majiyar ta cigaba da cewa, shugaba Buhari zai jingine batun tsuke yawan mukaman ministoci kamar yadda ya yi a zangon shi na farko.

A cewar majiyar, a wannan karon shugaba Buhari zai raba ma’ikatar ayyuka, lantarki da gidaje zuwa ma’aikatu uku, domin a samu damar gudanar da aiki a kowacce ma’aikata cikin sauki, yayin da ake sa ran shugaba Buhari zai fitar da ma’aikatar harkokin jiragen sama daga ma’ikatar sufuri, tare da maida ta ma’aikata mai cin gashin kan ta.

Leave a Reply