Zanga-zanga ta barke a Jihar Katsina, jim kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka.
Shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa, tafiyar shugaban Buhari daga Kofar-Kaura ke da wuya, wasu fusatattun matasa su ka kau kan titi su na ambaton “Ba ma yi, ba ma yi”, lamarin da ke nuni da cewa matasan su na fusace da gwamnatin shugaba Buhari.
Wani ganau ya ce, bayan shugaba Buhari ya kaddamar da aikin, wasu mutane da ba a san ko su wanene ba su ka fito daga cikin unguwannin da ke kusa da wurin su ka yi ta fadin ‘Ba ma yi’, tare da jifar motocin jami’an tsaro da wadnda ke dauke da tutar jam’iyyar APC da kuma kona tayoyi.
Bayan ‘yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa, shuga ba Buhari ya sake nausawa wani yankin domin kaddamar da wasu ayyuka.