Home Labarai Zanga-Zanga: Amnesty Ta Ce An Tsare Fiye Da Mutum 1000 A Najeriya

Zanga-Zanga: Amnesty Ta Ce An Tsare Fiye Da Mutum 1000 A Najeriya

49
0
Amnesty International
Amnesty International

Amnesty, ta bayyana cewa sama da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 1,000 ne ke tsare a hannun hukumomin Najeriya sakamakon shiga zanga-zangar ta baya

Zanga-zangar wadda aka gudanar tsakanin ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu sassan ƙasa,

inda aka samu rahotannin sace-sace da lalata kadarorin gwamnati a wasu jihohi.

Hukumomin tsaro a Najeriyar sun ce sun kama mutane da dama da ake zargi da hannu a yamutsin,

to sai dai a cewar kungiyar ta Amnesty International, mutanen da aka kama ;yan ba ruwan mu ne.

Daraktan kungiyar a Najeriya Malam Isa Sanusi, ya ce an kama mutane mutum 632 a Jihar Kano,

yayin da kuma a Sokoto an kama mutane za su kai 109 sannan kuma a Jihar Borno an kama mutum sama da 100.

Ya ce a Bauchi ma an kama mutane sannan kuma sun samu labarin cewa Kaduna ma an kama mutane da za su kai 70,\

a Katsina ma mutum 70 aka kama.

Leave a Reply