Ana ci gaba da zama cikin fargaba a faɗin duniya game da tattaunawar da kasar Mali ke yi da wani kamfani mai zaman kansa na sojojin Rasha mai suna Wagner group.
To sai dai wasu ƴan Mali da dama na ganin sojojin Rashar ba za su iya maye gurbin dakarun Faransa a kwanan nan ba.
An fara sanin ƙungiyar ne a 2014 lokacin da ta mara wa ƴan awaren da ke goyon bayan Rasha a rikicin gabashin Ukraine.
Tun bayan nan, ta yi aiki da ƙasashe ciki har da Syria da Mozambique da Sudan da Libya da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.
A shekarar 2013, an yi wa sojojin Faransa babbar tarba lokacin da suka isa Mali bayan da masu tsattsauran ra’ayi suka ƙwace wani tawaye sannan suka yi barazanar ƙwace iko da gaba ɗaya ƙasar.
Amma kwanan nan Shugaba Emmanuel Macron ya ce zai janye rabin yawan dakarun Faransa masu ƙarfi 5,000, kuma hakan ya zaburar da Firai Ministan Mali Choguel Maiga ya zargi faransa da watsar da ƙasarsa.
Wannan ya haifar da zazzafan martani daga Faransa, inda Ministan Rundunar Sojojinta Florence Parly ta zargi gwamnatin Mali da “yin dumu-dumu da jinin sojojin Faransa”.
You must log in to post a comment.