Home Labarai Zan Yi Shugabanci Cikin Ƙas-Ƙas Da Kai – Zaɓaɓɓen Shugaban Senegal

Zan Yi Shugabanci Cikin Ƙas-Ƙas Da Kai – Zaɓaɓɓen Shugaban Senegal

51
0

Zaɓaɓɓen shugaban kasar Senegal Bassiorou Diomaye ya yi
alƙawarin yin mulki tare da ƙan-ƙan da kai da kuma nuna
gaskiya.

Diomaye ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan zaɓen shugaban ƙasar da a ka yi ranar Lahadi.

Babban abokin hamayyar sa Faye daga jam’iyya mai mulki Amadou Ba tuni ya amince da shan kaye abin da ya sa Faye mai shekaru 44 ya zama shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a tarihin ƙasar ta Senegal.

Ya kara da cewa, zaɓen shi da a ka yi ya nuna cewa, al’ummar Senegal sun amince su tsame kansu daga abubuwan da su ka faru a baya, kamar yadda ya faɗa wa ƴan jarida a jiya Litinin.

A karshe Diomaye ya bayyana ɗaya daga cikin manyan ƙudurorinsa a matsayin shugaban ƙasa na haɗa kan ƴan kasar sakamakon yadda a ka shafe tsawon shekara uku a na tashin hankali da kuma rikicin siyasa a fadin ƙasar.

Leave a Reply