‘Yan bindiga sun mika wa gwamnatin jihar Zamfara bindigogi guda 216.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle Maradun, ya ce yawancin bindigogin da ‘yan ta’addan suka mika wa gwamnati kirar AK47 ne.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na gwamnan, Yusuf Idris, ya fitar a garin Gusau, gwamna Matawalle ya ce da dama daga cikin ‘yan bindigar da suka hana jihar zama lafiya sun tuba daga ayyukan ta’addanci.
Matawalle ya ce ‘yan bindigar sun maida wa gwamnati bindigogi da sauran makaman ne ta hannun wasu tubabbun ‘yan ta’adda, da suka lashi takobin taimaka wa gwamnatin jihar a kokarin ta na maido da zaman lafiya bayan sun tuba daga aikata miyagun laifuffuka.
Sanarwar ta ce, gwaman ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon, a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.
A cewar sanarwar, Matawalle, ya bayyana ziyarar Gowon a matsayin karramawa gare shi, tare da neman shawara daga gare shi a kan yadda gwamnatin sa za ta kawo karshen ta’addancin ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara.