Home Labaru Zamfara: Sabon Gwamnan Ya Sadaukar Da Albashinsa Ga Gidan Marayu

Zamfara: Sabon Gwamnan Ya Sadaukar Da Albashinsa Ga Gidan Marayu

616
0
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce zai sadaukar da rabin albashinsa ga gidan marayu na garin Gusau, babban birnin jihar.

Matawalle, ya bayyana hakan ne a wata ziyarar  bazata da ya kai gidan marayun, wacce kuma ita ce ta kasance ziyarar sa ta farko a wajen gidan gwamnati.

Ya kara da cewar daga lokacin da za a fara biyan sa  albashi a matsayin gwamna, ya bada umarnin a tura rabinsa zuwa gidan marayu, saboda yanzun ya zama uba ga duk yaran dake gidan zai ci gaba da kulawa da walwalar su daga wannan karamar sallar.

Ya tabbatar da cewar zai yi amfani da kudinsa domin dinka wa marayu tufafi da naman da za su ci, da kuma duk wani abu da zai saka su farin ciki a yayin bikin sallah.

Gwamnan ya ce zai taimaka wa kungiyar ‘yan jaridu ta NUJ tare da kulla mu’amala mai kyau da amfani da ita, kuma zan tabbatar da samar wa da kungiyar hanyoyin samun kudin shiga.

Leave a Reply