Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zamfara: Gwamnati Ta Kwace Kayan Abinci Da Man Fetur Da Aka Yi Yunkurin Kai Wa ‘Yan Fashin Daji

Yan bindiga

Gwamnatin jihar Zamfara, ta ce ta kama wasu motoci dauke da kayan abinci da ababen sha da kuma man fetur da ake yunkurin kaiwa sansanonin ‘yan ta’adda a jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma tabbatar da kama wasu mutane 100 da suka karya dokar kullen da aka sanya a fadin jihar domin yaki da ta’addanci.

Sakataren kwamitin ayyuka a bangaren tsaro na jihar Abdulrasheed Haruna, ya bayyana wa manema labarai haka a Gusau, inda ya ce gwamna Matawalle ya kafa wani kwamiti na musamman domin tabbatar da cewa an kiyaye dokar.

A ranar 26 ga watan Augusta da ya gabata ne, gwamnan jihar ya sanya hannu a dokar, wadda ke da alaka da sashin kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999.

Da ya ke sanya hannu a kan dokar, gwamnan Matawalle ya ce, ya yi aiki ne da karfin ikon da sashi na biyar sakin layi na 2 da sashi na 176 sakin layi na 2 da kuma sashi na 315 sakin layi na 2 na kudun tsarin mulkin Nijeriya suka bayar.

Exit mobile version