Rahotanni sun nuna cewa an kashe kimanin mutane 18 a wani hari da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Sarkin Tsafe Muhammad Bawa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin dan majalisa mai wakiltar Gusau da Tsafe Kabir Mai-Palace, ya ce mutane 18 ne aka kashe a harin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya ce sarkin wanda ya yi wa dan majalisar godiya da ziyarar da ya kai da kuma nuna damuwarsa akan lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari a garin Bamamu, Danmale da kuma kauyen Sako kan babura guda 50 kuma suka rika harbin kan mai uwa da wabi.
Shi ma a lokacin da yake magana dan majalisar Kabir Mai-Palace, ya bayar da taimakon kudi da katifu ga mutanen da abinda ya shafa.
You must log in to post a comment.