An kama wasu ‘yan Nijeriya biyu a Amurka, bisa zargin damfara da sauran laifuffukan da su ka kunshi dala dubu 25 na kudaden tallafin da ake ba marasa aiki.
Wata majiya ta ce, mutanen biyu da su ka hada da Olushola Afolabi da Olugbeminiyi Aderibigbe, ana zargin su da damfarar ma’aikatar tsaron ma’aikata da gwamnatin Amurka a shirin inshorar tallafa wa masara aikin yi.
Majiyar ta ce, mutanen su na aiwatar da damfarar ne ta hanyar takardun shaidar bogi da su ka kirkira, wanda ke ba su damar tura miliyoyin daloli na tallafin marasa aiki zuwa asusun bankin da su ke kula da shi, kamar yada gwamnatin Amurka ta shaida a takardun da ta gabatar kan mutanen da ake zargi.
Ana dai zargin mutanen da aikata damfarar ne tsakanin watan Oktoba na shekara ta 2020 zuwa Yuni na shekara ta 2021.