Ministan yada labarai Al’adu’, Lai Mohammed, ya cashe tare da fitacciyar mawakiya Teni a wajen wani taro da kamfanin Agip Oil ya shriya a birnin Fatakwal na jihar Rivers kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Wata majiya ta ce, Ministan ya nuna wa matasa cewa shi ma ba za a bar shi a baya ta fuskar walawa ba, linda ya nuna wa matasan cewa shi ma ya iya rawa.
Al’ummar da su ka hallarci taron da mafi yawancin su matasa ne, sun yi ta tafi da mamakin ganin ministan ya na tika rawa, yayin da wasun su ke daukar sa hotuna da bidiyo da wayoyin na sallula.
Mahalarta
taron da dama dai na ganin cewa, lamarin alama ce da ke nuna ministan shi ma na
matasa ne, kuma ba ya da girman kai kuma shi mutum ne mai son annashuwa da
walwala.