Home Labaru Zaman Lafiya: Majalisar Wakilai Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Saki El-Zakzaky

Zaman Lafiya: Majalisar Wakilai Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Saki El-Zakzaky

682
0
Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19
Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19

Rahotanni na cewa, Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta saki shugaban kungiyar ‘yan Shi’a kamar yadda wasu kotuna su ka bada belin sa a baya.

Majalisar ta amince da wannan kuduri ne, kwana daya bayan taho-mu-gamar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakazaky a harabar majalisar, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

Mai magana da yawun majalisar wakilai na riko Abdurrazak Namdas ya shaida wa manema labarai cewa, a matsayin su na wakilan jama’a, su na ganin ya dace a saki El-Zakzakky domin wanzar da zaman lafiya.

Idan dai za a iya tunawa, tun a shekara ta 2015 ake tsare da Sheikh Zakzaky, bayan wani hari da jami’an tsaro su ka kai wa magoya bayan sa a Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.Namdas ya cigaba da cewa, wannan ne ya sa ‘yan majalisar su ka nuna cewa tun da har ‘yan Shi’a sun dade su na zuwa nuna rashin jin dadin su ya kamata a saurare su.�2}w<2�

Leave a Reply