Majalisar dokoki ta jihar Kaduna ta amince da dokar sanya ido a kan harkokin wa’azi a fadin jihar.
Dokar wadda ta fara aiki a ranar Juma’r da ta gabata, ta maye gurbin dokar wa’azi ta shekara ta 1984 da aka samar.
A shekara ta ne 2016 aka gabatar wa majalisar da dokar, inda ba ta amince da ita ba sai a daidai lokacin da ta ke zaman ta na karshe kafin kafa wata sabuwar majalisar.
A baya dai dokar ta sha suka daga kungiyoyin addinai da wasu daidaikun mutane da ke ganin za a tauye wa masu wa’azi fayyace gaskiya.
Sai dai a lokacin da ta gabatar da kudurin ga majalisar a shekara ta 2016, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta yi hakan ne saboda samun daidaito da fahimtar juna da kuma zaman lafiya a tsakanin addinai.
Dokar dai ta kunshi kafa kwamitin kula da hadin kan addinai a matakin jiha da kananan hukumomi, inda za su rika tantance malaman da za su ba lasisin gudanar da wa’azi a fadin jihar.