Home Labaru Zabukan Bayelsa Da Kogi: An Tura ‘Yan Sanda Fiye Da Dubu 66...

Zabukan Bayelsa Da Kogi: An Tura ‘Yan Sanda Fiye Da Dubu 66 Domin Samar Da Tsaro – Adamu

478
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban hukumar ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu, ya ce hukumar za ta tura jami’an ‘yan sanda 66 da dari 341 domin samar da tsaro a ranar 16 ga Nuwamba, wato ranar da za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa.

Adamu ya bayyana hakan ne a taron kwamitin tabbatar da tsaro a zabukan, wanda shugaban hukumar INEC ta kasa farfesa  Mahmood Yakubu ya shirya a Abuja.

Muhammad Adamu ya ce za a tura ‘yan sanda dubu 31,041 a jihar Bayelsa, kana kuma a tura dubu 35,200 zuwa jihar Kogi, sannan ya ce hukumar ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a wadannan ranakun zabe.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma ce, hukumar su na sane da kalubalen tsaro a jihohin biyu kuma tuni saun samar da  abubuwan da ake bukata domin dakile rashin tsaro a jihohin.

Adamu ya ce, hukumar za ta tabbatar da tsaron ma’aikatan INEC da kayayyakin su, sannan kuma za su kare dukkanin rumfunan zabe da babban bankin Nijeriya CBN da ake ajiye kayayyakin zabe.

Leave a Reply