Home Labarai Zaben ‘Yan Majalisa: ‘Yan Hong Kong Sun Kada Kuri’a

Zaben ‘Yan Majalisa: ‘Yan Hong Kong Sun Kada Kuri’a

204
0
Al'ummar Hong Kong sun fara jefa kuri'a a karon farko tun bayan da China ta yi sauye-sauye ga tsarin siyasar yankin.

Al’ummar Hong Kong sun fara jefa kuri’a a karon farko tun bayan da China ta yi sauye-sauye ga tsarin siyasar yankin.

Sai dai duk ‘yan takara sun samu amincewar wani kwamiti da ke goyon bayan China kafin tsayawa takara.

Su kuma ‘yan adawa sun kaurace wa zaben kwatakwata.

Ana hasashen cewa ba za a fito jefa kuri’a sosai ba duk da shugabar gwamnatin Hong Kong din Carrie Lam ta ce ya yi wuri a yanke hukunci.

Carrie Lam ta ce da ma gwamnati ba ta yi hasashen adadin masu fitowa wannan zabe ba da kuma wanda ya gabace shi saboda abubuwa da dama ka iya tasiri wajen fitowar jama’a ko akasin haka.

A lokacin da ta jefa kuri’arta, shugabar ta bayyana sauye-sauyen da China ta kawo musu a matsayin ci gaba.

Leave a Reply