Home Labarai Zaben Shugabanni Ya Raba Kawunan Gwamnonin Jam’Iyyar APC

Zaben Shugabanni Ya Raba Kawunan Gwamnonin Jam’Iyyar APC

50
0

Kawunan Gwamnonin jam’iyyar APC sun rabu, dangane da
lokacin da za a shirya zaben shugabannin jam’iyya na kasa da ake sa ran zai gudana a watan Fabrairu na shkara ta 2022.

A karshen shekara ta 2021 ne wasu shugabannin jam’iyyar su ka
gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda aka amince a
gudanar da zaben a watan Fubrairu, amma ba a tsaida rana ba.

Yanzu haka dai, wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC sun hura
wuta, inda su ke son kwamitin rikon kwaryan da Mai Mala Buni
ke jagoranta ya sake dage lokacin yin zaben na kasa.