Kotun sauraren karar zaben shugaban kasa da jam’iyyar PDP da dan takaran ta Atiku Abubakar su ka shigar kan zaben shekara ta 2019, zai ci gaba da zama a ranar Litinin mai zuwa.
Wannan dai ya na ne, a daidai lokacin da bayanai ke nuna cewa shugabar kotun daukaka kara Zainab Bulkachuwa ta nada wanda zai jagoranci sauran alkalai 5 da ke sauraren shari’a a madadin ta.
A baya dai masu shigar da kara sun tunatar da mai shari’a Bulkachuwa cewa, ta zabo wanda zai maye gurbin ta domin gudanar da shari’ar a kan lokaci.
Bulkachuwa dai ta janye daga ci-gaba da jagorantar shari’ar ne a ranar 22 ga watan Mayu, bayan rashin tabbas da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku su ka nuna a kan adalcin ta.