Home Labaru Zaben Shugaban Kasa: Hukumar Zabe Ta Ce Shaidun Atiku Sun Gama Yi...

Zaben Shugaban Kasa: Hukumar Zabe Ta Ce Shaidun Atiku Sun Gama Yi Ma Ta Aiki

1191
0

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta shaida wa kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa cewa, babu bukatar ta gabatar da shaidu domin kare kan ta, saboda shaidun da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya gabatar sun gama wanke ta daga duk wani zargi da masu kara ke yi mata.

Atiku da jam’iyyar PDP dai su na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na shekara ta 2019, wanda hukumar zabe  ta bayyana shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara.

Kotun dai ta cigaba da zaman ta ne a ranar Litinin, domin hukumar zabe ta fara kare kan ta bayan masu kara sun kammala gabatar da korafin su da shaidu 62 a gaban kotun.

Babban lauyan hukumar zabe Yunus Usman, ya ce ba dole ne su gabatar da wata shaida domin kare kan sub a, saboda shaidun da masu kara su ka gabatar sun gama wanke hukumar zabe daga amsoshin tambayoyin da su ka bada lokacin da ya yi masu tambayoyi.

Kotun dai ta daga zaman sauraren karar zuwa ranar Talata domin fara sauraron lauyan da ke kare shugaba Muhammadu Buhari Cif Wole Olanipekun.

Leave a Reply