Rahotanni na cewa, ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar APC, sun yi fatali da tsarin zaben fidda gwanin da uwar jam’iyyar ta kasa ta ce a gudanar a cikin sirri.
‘Yan takarar da yawan su ya kai 20 dai sun sanar da haka ne a cikin wata takadar korafin rashin amincewa da su ka aike wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Adams Oshiomhole kamar yadda daya daga cikin su Muhammed Ali ya bayyana wa manema labarai a Abuja.

Muhammed Ali, ya ce sun je helkwatar APC ne don kawai su nuna rashin amincewar su da tsarin zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta ce a gunadar a jihar Kogi.
Ya ce ba su amince a yi zaben fidda-gwanin a asirce ba, su na so a kafa kwamitin zabe mai zaman kan sa ya shirya zaben, ta yadda za a bar duk mai sha’awar fitowa takara ya shiga zabe.
Idan
dai ba a manta ba, a ranar 5 Ga Yuli ne uwar jam’iyyar APC ta ce a yi zaben
fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Kogi a asirce.
You must log in to post a comment.