Home Labaru Zaben Kogi: ‘Yan Bangar Siyasa Sun Kona Sakatariyar Jam’iyyar SDP A Lokoja

Zaben Kogi: ‘Yan Bangar Siyasa Sun Kona Sakatariyar Jam’iyyar SDP A Lokoja

800
0

Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne, sun kona sakatariyar jam’iyyar SDP da ke birnin Lokoja na jihar Kogi.

Sakatariyar SDP dai  ta na fuskantar sakatariyar karamar hukumar Lokoja ne a kewayen Dandalin Paparanda.

Tun farko an kai wa sakatariyar SDP hari ne a ranar Lahadin da ta gabata, bayan wasu mutane da ba a sani ba sun fasa tagogi da kofofin ta, inda su ka lalata sauran kayayyakin yakin neman zabe da ke sakatariyar.

Jam’iyyar SDP ta yi zargin cewa, akwai wani shiri da ake yi na kai wa ayarin ‘yar takarar gwamnan ta Barista Natasha Akpoti hari gabannin zaben ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply