Home Labaru Zaben Kogi: PDP Ta Ce APC Na Kulla Makircin Dage Zabe

Zaben Kogi: PDP Ta Ce APC Na Kulla Makircin Dage Zabe

398
0

Kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa, akwai wani makirci da ake kullawa domin dage zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba.

PDP ta zargi jam’iyyar APC da gwamnatin jihar Kogi da shirya wannan makarkashiya ne na saura kasa da mako gudana a gunadar sa zaben.

Bayanin haka dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan labarai na jam’iyyar Austin Okhai ya aikewa manema labarai, inda ya kara da cewa jami’iyyar APC da gwamnatin da Yahaya Bello su na nan suna shirya makirci gabannin wannan zaben.

Okhai ya ce PDP ta shirya cewa APC ce za ta zo ta uku a zaben, don haka suke kulla makirci domin jinkirtar da tsarin zaben, wanda haka ya sa kungiyar yakin neman zaben PDP ta roki hukumar INEC da kada ta yarda da duk wani yunkuri da zai saba abunda mutanen jihar ke tsammani.

Jam’iyyar ta ce magoya bayanta da masu zabe ‘yan asalin jihar sun taso daga wurare da ke nesa da kusa domin samun damar zabar dan takarar PDP, wand adage zaben  zai shafi sakamakon wannan zaben.