Home Labaru Zaben Kogi: Babu Dan Takarar Da Za A Maida Wa Kudin Sa...

Zaben Kogi: Babu Dan Takarar Da Za A Maida Wa Kudin Sa – Oshiomhole

408
0
Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur
Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar APC Ta Kasa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Kwamred Adams Oshiomhole, ya wancakalar da zancen yiwuwar maida wa ‘yan takarar da su ka fadi zaben fidda gwanin kujerar gwamnan jihar Kogi da ya gudana kudaden su.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Oshiomhole ya ce ba a tantance bakwai daga cikin ‘yan takara 16 da su ka yanki fom a kan naira miliyan 22 da rabi 5 ba saboda wasu dalilai, amma an tantance sauran mutane tara, ciki kuwa har da Gwamna Yahaya Bello da ya lashe tikitin takarar jam’iyyar.

Oshiomhole ya ce jam’iyyar APC ta na tafiyar da ayyukan ta bisa tsarin dokoki, don haka idan akwai al’amuran da ya kamata a tattauna a kai, al’amuran cikin gida ne kuma bai kamata a bayyana wa manema labarai ba. Ya ce duk wadanda ba su samu nasara a zaben ba, sun bada tabbacin cewa ba za su kalubalanci sakamakon zaben ba a kotu, amma za su yi aiki don ganin nasarar jam’iyyar a lokacin zabe.

Leave a Reply