Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ba zababben gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin sa Nasiru Yusuf Gawuna da zababbun ‘yan majalisar jihar 27 shahadar lashe zabe.
Sai dai ‘yan majalisar 13 da na jam’iyyar PDP ba su halarci taron ba, wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha.
Da ya ke gabatar da shahadar, kwamishinan zabe na kasa mai kula da Kano da Katsina da Jigawa Injiniya Abubakar Nahuche, ya bukaci ‘yan siyasa su kasance masu alkawari kada kuma su dauki siyasa a matsayin a mutu ko a yi rai. Ya kuma bukaci wadanda su ka lashe zaben su tabbatar da cewa damokradiyar Nijeriya ta bunkasa.
You must log in to post a comment.