Kafofin yada labaran Isra’ila sun sanar da cewar, Firaminista Benjamin Netanyahu, ya kama hanyar lashe zaben kasar wanda zai bashi damar yin wa’adi na 5.
Tuni Netanyahu, da abokin karawar sa tsohon shugaban sojin kasar Benny Gantz, suka bayyana samun nasara a zaben.
Bayan kammala kidaya kashi 97 na kuri’un da aka kada, sakamakon zaben ya nuna cewar Jam’iyar Likud ta Firaminista Benjamin Netanyahu, da kawayen ta sun samu tsakanin kujeru 65 daga cikin kujeru 120 dake Majalisar kasar, abinda zai basu damar samun nasara.
Ganin yadda zaben ya gudana da yadda ake tafiya kankankan tsakanin Netanyahu, da babban mai adawa da shi Benny Gantz, an dan samu shakku da kuma fargaba lokacin da aka fara bayyana sakamakon, abinda ya sa Netanyahu, da Gantz, kowa ya fito ya bayyana samun nasara.
Firaminista Netanyahu ya bayyana sakamakon zaben a matsayin gagarumar nasara, inda yake cewa ya fara tattaunawa da jam’iyyun kawance kuma gwamnatin sa zata zama na ‘yan ra’ayin rikau ne zalla.
Shi kuwa Benny Gantz, ya bayyana sakamakon a matsayin ranar tarihi, inda ya bukaci Netanyahu ya basu damar kafa gsabuwar gwamnati.
You must log in to post a comment.