Home Labaru Zaben Indonisiya: Jami’an Zabe Sama Da 270 Suka Mutu Yayin Kirga Kuri’a

Zaben Indonisiya: Jami’an Zabe Sama Da 270 Suka Mutu Yayin Kirga Kuri’a

252
0

Sama da jami’an zabe 270 ne suka mutu a kasar Indonisiya bayan sun tagayyara daga kirga kuri’un miliyoyin ‘yan kasar da suka jefa.

An bayyana cewa akasarinsu sun fara rashin lafiya ne sakamakon dogon lokacin da suka dauka suna kirga kuri’u.

Mai magana da yawun hukumar zaben kasar Arief Susanto ya bayyana cewa akwai kusan jami’an zabe 1,878 da suka fara rashin lafiya.

Irin wannan shine zabe na farko a kasar mai mutane kusan miliyan 260 inda aka hada zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisun tarayya na da na yankuna.

An bayyana cewa an hada zabukan ne lokaci guda domin saukakawa gwamnati wajen kashe kudade amma da alamu hakan ya sa jami’an zaben cikin wahala har wasu suka rasa ransu.

Kusan mutum miliyan 64 ne suka jefa kuri’unsu a rumfunan zabe kusan 800,000.

Gagarumar girgizar kasa ta auku a tsibirin Lombok na Indonisiya.