Home Labaru Zaben Gwamnan Kogi: Yahaya Bello Ya Ki Goyon Bayan Mataimakin Sa

Zaben Gwamnan Kogi: Yahaya Bello Ya Ki Goyon Bayan Mataimakin Sa

77
0

A yayin da Hukumar Zabe ta Kasa ta sanya 11 ga watan
Nuwamba a matsayin ranar zaben Gwamnan jihar Kogi,
Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya ke so ya gaje
shi.

Sai dai gwamnan ya shammaci jama’a, domin ba mataimakin sa Edward Onoja ba ne dan takarar sa, wanda ya kasance
tsohon shugaban ma’aikatan Yahaya Bello, daga baya gwamnan ya daga likkafar sa zuwa matsayin mataimakin gwamna bayan an tsige Achuba a shekara ta 2019.

A wani taron masu ruwa da tsaki da masu neman takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar APC su ka gudanar, Gwamna Yahaya Bello ya bayyana tsohon Odita-Janar na Jihar Kogi Usman Ododo a matsayin dan takarar sa.

Baya ga Adodo da Onoja, sauran wadanda su ka nuna sha’awar kujerar gwamnan sun hada da Mohammed Abdulkareem Asuku, da David Adebanji Jimoh da Asiwaju Ashiru Idris da Okala Yakubu.

Sai dai majiyoyi sun ce dukkan su sun janye wa Adodo bayan gwamnan ya bayyana shi a matsayin zabin sa.

Leave a Reply